JAN HANKALI GA IYAYEN YARA....




 A wannan rana ta juma'a muna cikin jajiberan Zaben Inconclusive ne a jahar Kano.


 Zanyi amfani da wannan dama nayi kira ga Iyayen mu Maza da Mata.

 Zanyi kiran ne bisa wani nazari da nayi dangane da mafiya yawan 'yan siyasar kasar nan sundauki wata dabi'ar amfani da 'ya'yan wasu a matsayin yan bangar Siyasa, a lokacin dasu nasu 'ya'yan suna can Kasashen ketare suna hutunsu wasun kuma suna Tsaftatcen karatu.

 Babban dalilin da yasani wannan rubutun shine naji wani Babban Dan siyasa a Jahar Kano yana kokarin tunzura yayanwasu ta hanyar turasu gurin zabe mafi hadari da bantsoro wai kuma yana fada musu cewa Kowannenku SECURITY NE. Hakama Kowannenku AGENT NE. Sannan kuma kowa yakare kansa.

 Amma duk wannan Umarnin da yake basu yayansa Suna MAROCCO suna Shagalinsu.

 Dan haka Iyayen mu Mata da Maza Ku kame yayanku kuja kunnensu,idan aka illata muki yaya baisan hanyar gidanku ba ballanta yayan naku.

 Ku za'a bari da wahala.

Shirin da yan siyasa sukayiwa wannan zabe bana wasa bane.

 Shirin da Jami'an Tsaro sukayiwa wannan zabe bana wasa bane.

C.P. M.Wakili shi kanshi dan kallone, domin iyayensa a aikine zasu jagoranci lamarin.

 Dan haka ina shawartarku lalle ku kame yayanku ku adanasu a cikin gida.


Nagode.

22/03/2019
Mukhtar Hashim Hotoro.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog