HABA KANAWA



Ga zahiri mai zai hadaku da gaibu, kuna dai ganin irin jajircewar da Gwamna Ganduje
keyi wajen inganta rayuwar kanawa da Kano tun zuwansa kan mulki a shekarar 2015, shin bakwa ganin cewa zuwan masu jajayen kawuna kano babbar masifar da zata mayar da Jiharku baya ne.

Ku kalli zahirin ayyukan da Gwamna Ganduje yayi muku daga manya manyan gadojin zamani zuwa sabbin titunan daya samar, ga manyan asibitoci guda biyu duk daya samar cikin kasa da shekara hudu, inganta harkar ilmi tare da samawa matasa ayyukanyi tare da bude makarantun koyawa matasa aikin dogaro dakai duk a zamanin Ganduje.

Ranar 23 ga watan March kanawa baku da zabin daya wuce Gwamna Ganduje don cigaba da ayyukan alheri tare da mutumta malamku ga kyakkyawar muamula cikin sanin ya kamata da gwamna Ganduje keda ita.

Karerayi ne kawai jagoran Kwankwasiyya yake muku, yana samun dama ba abun dazai sanya a gaba sai cin zarafin al'umma tare da karya tattalin arzikin jihar, burinsa kawai ya samu mulkin kano don dibar kudin kanawa yayi kamfen dasu a zaben 2023.

Comments

Popular posts from this blog