DALILINA
Lokacin da nike school madugu yayi wa iyayen mu retire haka kawai, ya kwashe kudin pension din su ya gina
kwankwasiyya city, wanda be amfane su ba. Seda muka yi 3 years bama zuwa school ni da qanne na duka. Neman yanda zamu ci abinci ake ba makaranta ba tukunna.
Yazo yace free education,a gurin registration aka ringa kallo fuska mu ba interview ba komai Ana saka mana non-indigene/non-Nigerian, suka ringa tura mutane central admin, inda aka sace min kudi da laptop, tun 7 na safe har after magrib, gashi an sace kudin motar ma da zanje gida. Aka hana mu scholarship din da yake taimaka mana wurin kudin mota da siyan handout.
#Madugu158 ya tura wasu dalibai kasashen waje akan karatukan da muke dasu a makarantun mu na gida, Mu da muke Nigeria kudin Handout da kudin Mota ya gagare mu.
Ya biya musu kudin zuwa qasar waje su dayawa, maimakon a samu discount sabida suna da yawa, sai ma kudin da ya qaru, yaci riba dasu kenan?. Yace kudin 3 years ya biya, mesa da Ganduje ya hau ya ga kudin 1 year aka biya, GANDUJE ne ya biya sauran, wasu kuma iyayen su suka biya musu, wasu har bara sunyi, wasu aikatau. To sauran kudin 2 years din me tsula158 yayi da su?
Dukkan ayyukan da wani shugaba ya tafi ya bari babu wanda kwankwa158 ya qarasa, amma da GANDUJE yazo da na madugu158 da na Mallam Ibrahim Shekarau duk ya hada ya qarasa su, kamar asibitin Giginyu, Zoo ROAD kuma ya daura daga inda suka tsaya.
Ganduje baya siyasa ta zagi, sai ta barkwanci, baya wulaqanci, cin mutunci manya, malamai, tunzira matasa zuwa fitina irin su saukale, agent, security. Hasalima yana girmama mutane.
Yanzu gashi a PDP baa yi primaries ba ya dauka takara ya bawa surinkin sa, yaci zalin sauran yan takarar, anzo zabe yace kowa agent, an samu over voting daga wurin su, an samu invalid vote sama da 100k sannan yanzu suna alqunut wai an zalunce su, suna zagin shugaban qasa da babu ruwan shi, suna cewa malamai sunqi magana akai bayan sunce in malami ya shiga sabgar su zasu dura mai ashariya.
KA RIQE DALILINKA NA RIQE Allah baya bacci, yana kallon komai... Allah baya zalunci #GANDUJEkawai
Comments
Post a Comment